On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Sanatocin APC 22 Sun Janye Shirinsu Na Ficewa Daga Jam'iyyar

SANATOCIN APC

Sanatocin jam’iyyar APC 22 da suka harzuka dangane da yadda sakamakon zaben fidda gwaninsu ya kasance, harma suke shirin ficewa daga cikin jam’iyyar, sun jingine aniyar tasu.

Hakan na zuwa  ne a yayin da sanatacin suka gana da shugaban Kasa Muhammadu Buhari yau a Abuja.

Jagoran Sanatocin, Sanata Orji Kalu   wanda ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa da aka fitar, Ya baiyana cewa  Sanatocin sunji  rashin dadin yadda  aka gudanar da zaben fidda gwanin.

Da yake gabatar da jawabi a yayin ganawar da suka yi, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci sanatocin  dasu janye  shirinsu  na ficewa daga cikin jam’iyyar.

Shugaban yace sauyin sheka babbar barazana ce ga rinjayen da jam’iyyar APC ke dashi a majalisar Dokoki ta kasa.