On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Sarkin Musulmi Yayi Ganawar Sirri Da Gwamna Wike

GWAMNA WIKE DA SARKIN MUSULMI

Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, Ya karbi bakuncin Mai Alfarma Sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na Ukku.

Sarkin musulmin ya ziyarci gidan gwamnan dake Ada George dake birnin Fatakwal, jim kadan bayan ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa dake birnin na Fatakwal.

Rahotanni sun baiyana cewa jagororin biyu sun yi ganawar sirri a tsakaninsu.

ATIKU ABUBAKAR DA GWAMNA WIKE

Basaraken yaje  birnin Fatakwal ne domin  bude babban taron kungiyar mata musulmi na kasa FOMWAN karo na 37.

More from Labarai