Kungiyar SERAP mai fafutukar kare hakkokin tattalin arziki da tabbatar da gaskiya da rikon amana ta shigar da kara a kan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), bisa zargin cewa ta gaza binciken zarge-zargen da ke cewa gwamnonin da aka zaba a karkashin jam'iyyar APC sun karkatar da naira biliyan 800 daga kudaden Asusun Tarayya (FAAC) domin harkokin siyasa da yakin neman zabe.
A cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan kungiyar, Kolawole Oluwadare, ya fitar a ranar Lahadi, SERAP ta ce an shigar da karar ne a makon da ya gabata a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Kungiyar ta ce, bisa rahotannin kafafen yada labarai, gwamnonin APC na bayar da gudunmawar wata-wata daga kudaden FAAC da suke karba zuwa wani asusun yakin neman zabe domin tallafawa yakin neman sake zaben Shugaba Bola Tinubu a shekarar 2027.
SERAP ta kuma bayyana cewa ta bukaci kotu ta umarci INEC ta gudanar da bincike kan zarge-zargen, ta tilasta wa jam'iyyar APC da gwamnoninta su bayyana cikakken bayani kan kudaden da aka bayar, sunayen masu bayar da gudunmawar da kuma asalin kudaden, tare da binciken ko jam'iyyun siyasa da 'yan takara sun bi tanadin sashe na 91 na Dokar Zabe dangane da kudaden yakin neman zabe, tana mai cewa zarge-zargen na haifar da damuwa kan gaskiya da adalci a tsarin zabe tare da barazana ga dimokuradiyya.
Comments
Add a comment