On Air Now

ZANGON MARAICEN LAHADI

6:00pm - Midnight

SERAP Ta Kai Karar Shugaban Kasa Saboda Kin Bin Umarnin Kotu Kan Cigaba Da Amfani Da Tsohon Kudi

Kungiyar nan mai rajin kare hakkin dan adam da kuma tabbatar da adalci a hukumomi da ma’aikatun gwamnati SERAP ta kai karar Shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda kin yin biyayya ga umarnin da kotu ta bayar, inda ya ya haramta yin amfani da tsohuwar naira 500 da kuma dubu 1.

Lauyoyin  kungiyar Ebun-OluAdegboruwa da Kolawole Oluwadare ne suka shigar da karar a madadin  kungiyar ta  SERAP a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja.

SERAP na neman kotu ta tantance ko umarnin da shugaba Buhari ya bayar na haramta yin amfani da tsohuwar naira  500 da da  dubu  1  bai dace  da tsarin kundin tsarin mulkin kasa  da kuma umarnin da kotun koli ta bayar,

SERAP na kuma neman   kotun ta bada wani  umarni na wucin gadi da zai hana shugaba Buhari da  Babban bankin kasa  CBN ci gaba da aiwatar da umarnin hana  yin amfani da  tsofaffin takardun kudi.