Shahararren jarumin fina-finan Nollywood kuma tsohon mai watsa shirye-shiryen rediyo, Cif Pete Edochie, ya rasu yana da shekaru 79 a duniya bayan fama da cutar sankarar mafitsara.
Dansa, Leo Pete Edochie, ne ya sanar da rasuwar tasa a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamban 2026, inda ya ce mahaifinsa ya rasu da misalin karfe 12 da rabi na dare a jihar Enugu.
Iyalan marigayin sun bayyana shi a matsayin miji, uba, dan uwa kuma jigo a cikin al'ummarsa da za a dade ana tunawa da shi, tare da cewa za su sanar da shirye-shiryen jana'izarsa nan gaba.
Pete Edochie ya yi fice sosai a shekarar 1987 bayan taka rawar Okonkwo a fim din talabijin da aka shirya daga littafin Things Fall Apart na marubuci Chinua Achebe, inda daga bisani ya zama daya daga cikin fitattun jaruman masana'antar fina-finan Nollywood, tare da fitowa a fina-finai da dama tsawon shekaru.
Comments
Add a comment