Rahoto: Nura Haruna Mudi Al'ummar bayan gidan Sarkin Dutse yamma da ke Dorayi Karama a karamar hukumar Gwale ta Jihar Kano sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da dukkan hukumomin da abin ya shafa da su kai musu dauki, suna masu gargadin cewa dubban mazauna yankin na ci gaba da rayuwa cikin barazanar rasa rayuka da dukiyoyinsu sakamakon matsalar ambaliyar ruwa da ta ki ci ta ki cinyewa tsawon sama da shekaru ashirin.
A wata sanarwar manema labarai da Dr. Yusuf Ibrahim ya sanya wa hannu a madadin Gamayyar Mazauna Bayan Gidan Sarkin Dutse Yamma, al'ummar sun ce duk lokacin damuna yankin na rikidewa zuwa kogi, inda ambaliyar ruwa ke mamaye gidaje da lalata hanyoyi da rushe gine-gine da kuma jefa iyalai cikin mawuyacin hali.
Sun ce matsalar ta samo asali ne daga rashin wadatar babbar magudanar ruwa da ke karbar ruwan sama da kuma ruwan da ke gangarowa daga sassa daban-daban na Dorayi.
A cewar sanarwar, tarihin yankin ya shaida irin barnar da ambaliyar ta yi musamman a shekarun 2002, 2013 da kuma 2026, inda aka yi asarar rayuka, aka lalacewar gidaje da kadarori, tare da tilastawa iyalai da dama barin gidajensu domin tsira.
"Ba yau muka fara fuskantar wannan iftila'i ba. Sama da shekaru ashirin kenan muna rayuwa cikin fargabar ambaliya, muna rasa dukiyoyinmu, wasu kuma suna rasa rayukansu, amma har yanzu ba a samar mana da mafita ta dindindin ba."
Kungiyar ta ce matakin da wasu matasa ke dauka na toshe bakin magudanar ruwa a wasu lokuta ba ganganci ba ne ko kuma yunkurin karya doka, sai dai matakin kare kai da ya samo asali daga tsananin wahala da rashin samun mafita daga hukumomin da suka dace.
"Abin da mutane ke gani a matsayin laifi, a gare mu matakin neman tsira ne. Ba mu dauki wannan mataki don cutar da kowa ba, sai dai domin kare rayuka da gidajenmu daga bala'in da ya dade yana addabarmu."
Sai dai kungiyar ta amince cewa irin wadannan matakai bai kamata su kasance ba tare da kulawar hukumomi da kwararrun injiniyoyi ba, tana mai cewa mafita ta gaskiya ita ce gwamnati ta dauki matakin da ya dace cikin gaggawa.
"Abin da muke bukata shi ne fahimta, tausayi da kuma maganin tushen matsalar."
Mazauna yankin sun bukaci Gwamnan Jihar Kano da ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike na kwararru kan tsarin magudanar ruwa na yankin, tare da samar da matakan kariya na wucin gadi bisa ka'idodin aikin injiniya kafin a fara aiwatar da babbar mafita ta dindindin.
Har ila yau, sun bukaci a kira taron dukkan al'ummomin da matsalar ta shafa domin samar da mafita ta hadin gwiwa, sannan gwamnati ta gaggauta ginawa ko fadada babbar magudanar ruwa mai isasshen karfin daukar ruwa domin kawo karshen matsalar baki daya.
Kungiyar ta jaddada cewa tana goyon bayan doka da oda, tare da bayyana cewa manufarta ita ce kare rayuka da dukiyoyin kowa ba tare da jefa wata al'umma cikin hadari ba.
A wani sako ga matasan yankin, kungiyar ta bukace su da su ci gaba da kasancewa masu hakuri da bin doka, duk da irin wahalhalun da suke fuskanta.
Kungiyar ta ce lokaci ya yi da gwamnati za ta daina daukar wannan matsala a matsayin abin da za a ci gaba da jinkirtawa, tana mai gargadin cewa idan ba a dauki matakin gaggawa ba, ambaliyar ruwa na iya sake janyo asarar rayuka da dukiyoyi a damunar bana.
Comments
Add a comment