On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Shin Karfin Manchester City Da Real Madrid Ya Zo Daya Ne ?

Dan wasa Kevin De Bruyne ya farkewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester City kwallon da Real Madrid ta fara zura mata a raga a ranar Talata, a wasan da suka tashi 1 da 1

A wasansu na  zagayen  farko na gasar cin kofin zakarun Turai na UEFA, dan wasan tsakiyar Manchester City ya farke kwallon ne  a minti na 67.

Hakan ya faru ne bayan Vinicius Junior ya fara zura kwallo a ragar  mancheste  city  a zagayen farko  na wasan.

Manchester City ce ta mamaye wasan a farkon  amma Real Madrid ta karbe ragamar wasan  daga  baya.

 Manchester City za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan zagaye na biyu a ranar Laraba mai zuwa.