On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Shin Kayi 'Dinkin Sallah Kuwa?

TELA

A yayin da watan Ramadana ke kara nisa hankula kuma sun karkata daga siyayar buda baki zuwa siyayar sallah wanda yawanci yake da alaka da siyan sababbin kaya ga manya da yaran alummar musulmai.

Wakiliyarmu Jamila Seyoji Adam wacce ta lura da irin yanayin da ake ciki a birnin Kano ta labarto mana cewar an mayar da hankali zuwa kan teloli da sauran masu kwaliyar tufafi wadanda yanzu haka suke samun kulawa daga gurin alumma.

A wata tataunawa da Arewa Radio wata tale anan Kano da aka dade anan damawa da ita a harkar malama Aisha ta bayana cewartelolin yanzu suna samun aiyuka sosai sai dai rashin isasun kudi a hannu na taba sana’ar tasu

Amma kuma wasu teloli sun koka da matsalar rashin wutar lantarki da ake fuskanta a yawancin sassan jahar nan inda suka ce yawanci suna dogara ne da man fetur wanda a halin yanzu yake da tsada