On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Shirin N-Power Zai Dawo Da Sabbin Tsare-Tsare - Minista Betta Edu

Gwamnatin tarayya ta ce ana shirin yin garambawul ga shirin N-Power domin daukar karin masu amfana da kuma tabbatar da biyan alawus ba tare da bata lokaci ba.

Shirin na N-Power wani shiri ne da ke da nufin bunkasa fasahar matasa da bunkasa harkokin kasuwanci.

Ministar jin kai da kawar da fatara, Betta Edu ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi a Abuja.

Ministar ta ce za a sake kaddamar da shirin tare da sabon tsari da kumakudiri.

Ta ce ma’aikatar na shirin kafa cibiyoyin jin kai a fadin kananan hukumomi 774 a matsayin wani dogon buri na kawar da talauci a kasarnan.