On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Shiru Ba Tsoro Ba Idan Lokaci Yazo Wike Zai Fuskanci Kora Ba Dakatarwa Ba Daga Jam'iyyar PDP - Bwala

Tsohon mai magana da yawun Majalissar yakin neman zaben Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na 2023, Daniel Bwala, yace za'a kori ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike daga jam’iyyar PDP a lokacin da ya dace.

Bwala ya yi magana ne a gidan Talabijin na Channels a daren jiya, kwana guda bayan Wike, tsohon gwamnan jihar Rivers, ya sha alwashin cewa babu wanda zai iya korarsa daga jam’iyyar PDP…

Bwala ya ce shiru da jam’iyyar ke yi ba rauni ba ne, ya kara da cewa jam’iyyar ta san abin da take yi kuma a lokacin da ya dace ba wai kawai za a dakatar da Wike ba matakin zai kasance na kora daga PDP baki daya.