On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Shiye-shirye Sunyi Nisa Domin Fara Yakin Neman Zaben Tinubu/Shattima 2023 – Simon Lalong

Jam’iyyar APC ta ce shirye-shirye sun kusan kammala domin fara yakin neman zaben Tinubu da Shettima na shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.

Darakta-Janar na yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a 2023 gwamna Simon Lalong,  shine ya bayyana haka bayan ya duba kayayykin da aka samar a shalkwatar yakin neman zaben da ke Abuja.

Mai magana da yawun gwamnan Dr Makut Macham,  ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar jiya a Jos, yace sakataren kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, James Faleke, ya tarbi Lalong a shalkwatar.

Macham ya ce shugaban ya kuma gana da wasu ma’aikatan majalissar yakin neman zaben, a wani bangare na kokarin tabbatar da wata babbar tawaga ta yakin neman zaben.