On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Shugaba Buhari Na Najeriya Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Matakai Kan Sauyin Yanayi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira da a dauki matakin gaggawa kan sauyin yanayi daga manyan kasashen da suka ci gaba domin tunkarar matsalar sauyin yanayin a Afirka.

Buhari wanda ya samu wakilcin Ministan Muhalli, Mohammed Abdullahi ya yi wannan kiran a ranar Litinin a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi na COP27 na shekarar 2022.

Taron neman kawo sauyi da tsaftace Makamashi ya baiwa Najeriya dama don bayyana yunĆ™urin magance  yanayi da damuwar yanayi.

Saboda haka ya yi kira da a gaggauta daukar matakai daga kasashen da suka ci gaba wadanda ke fitar da mafi yawan hayakin da ke shafar yanayi a Afirka.