On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Shugaba Buhari Zai Kaddamar Da Aikin Hakar Mai A Yankin Arewa Maso Gabashin Najeiya - NNPC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da aikin hako man fetur a kogin Kolmani na II dake yankin Arewa maso gabas ranar talat mai zuwa.

Jami’an Kamfanin Man Fetur na NNPC  Limited sunce za a fara aikin hakar mai ka’in da na’in a kogin na Kolmani da ke cikin yankunan Bauchi da Gombe bayan kaddamarwa.

A watan Oktoba na shekarar 2019, kamfanin NNPC ya sanar da gano ma’adanar iskar gas a rijiyar Kolmani ta II. An dai gano tarin arzikin man fetur a jihohin biyu shekaru biyu da suka gabata.

Kararamin ministan man fetur na ƙasa  Timipre Sylva, yace  a gudanar da bikin fara tono man ranar Talata 22 ga watan da muke ciki na Nuwamba Inda shugaba Buhari tare da wasu daga cikin ministocinsa za su halarta.

Oil well 1

A shekarar 2016 ne kamfanin mai na ƙasar NNPC ya ƙaddamar da aikin binciko man fetur a arewacin ƙasarnan, abin da ya kai ga gano ɗimbim albarkatun man fetur ɗin a jihohin Bauchi da Gombe da Borno da kuma jihar Neja..