On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Shugaba kim Jon Un Zai Gana Da Vladimir Putin

KIM DA VLADIMIR

Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un na Koriya na shirin yin balaguro zuwa kasar Rasha a cikin wannan watan domin ganawa da shugaba Vladimir Putin, kamar yadda wani jami'in Amurka ya shaidawa manema labarai.

Jami'in ya ce shugabannin biyu za su tattauna kan yiwuwar baiwa kasar Rasha  makamai domin taimakawa yakin da take yi   a Ukraine.

Kawo yanzu dai ba a bayyana ainihin wurin da aka shirya ganawar  ba,  kuma babu wani karin haske kan wannan  rahoto da aka fitar.

Wasu Majiyoyi sun shaida wa jaridar New York Times cewa, mai yiwuwa shugaba  Kim Jong Un  zai yi  tafiyar ne a cikin jirgin kasa  mai sulke.

Yiwuwar ganawar ta zo ne bayan da fadar mulkin Amurika ta  White House tata ce ta samu sabbin bayanai da ke nuna cewa akwai  tattaunawar samar da  makamai tsakanin kasashen biyu.