On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Shugaba Tinubu Ya Bada Kwangilar Bincike Akan Bankin Najeriya CBN

Shugaba Bola Tinubu ya nada wani mai bincike na musamman Jim Osayande da zai binciki babban bankin kasa CBN da ayyukan da suka shafi gudanarwar bankin.

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban kasar kuma aka aikawa Obazee, babban jami’in hukumar bayar da rahoto kan harkokin kudi ta Najeriya.

Tinubu ya kuma aikewa Obazee kwafin umarninsa na dakatar da Godwin Emefiele amatsayin gwamnan  babban bankin.

Wannan ci gaban na zuwa ne a daidai lokacin da Emefiele ke fuskantar shari'a.

Yayin da Emefiele ke ci gaba da kasancewa a tsare  a hannun DSS a makon da ya gabata wata kotu ta bayar da belinsa amma hukumar ta sake kama shi nan take.