On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Shugaba Tinubu Ya Bada Umarnin Sake Nazari Kan Tallafin Naira Dubu 8 Ga Gidajen Talakawa Masu Rauni

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin a sake fasalta shirin bada kudi Naira dubu 8 da aka tsara domin  tallafi ga gidajen Talakawa da sukafi rauni a Najeriya.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Dele Alake, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce umarnin ya biyo bayan sauraron ra'ayoyin da 'yan Najeriya suka bayyana akan tsarin.

Alake ya ce shugaban kasar ya kuma bayar da umarnin a gabatarwa ‘yan Najeriya gaba daya tsarin tallafin da gwamnati zata bayar domin ba iya shirin tallafin kudi ba ne kadai a jimillah tsare-tsaren Rage radadin.

Alake ya ce shugaba Tinubu amatsayin jagora mai sauraron Jama’arsa ya kuma ba da umarnin a gaggauta sakin takin zamani da hatsi ga manoma da gidaje miliyan 50 a fadin jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja.