On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Shugaba Tinubu Zai Yiwa 'Yan Najeriya Jawabi

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga ‘yan Najeriya a yau Litinin, 31 ga Yuli, 2023 da karfe 7 na yamma.

An tabbatar da jawabin ta cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban shawara kan ayyuka na musamman da sadarwa Dele Alake ya fitar.

Sanarwar ta umarci gidajen Talabijin da gidajen rediyo da sauran kafafen yada labarai na zamani da su jona jawabin daga gidan talabijin na kasa NTA  da gidan Rediyon tarayya.