On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Shugaban Hukumar Kula Da Aiyukan Yansanda Ta Kasa Musliu Smith Yayi Murabus

MUSLIU SMITH

Shugaban Hukumar kula da ayyukan yansanda ta kasa Alhaji Musiliu Smith ya tabbatar da ajiye shugabancin hukumar da safiyar yau.

Mai magana da yawun hukumar Ikechukwu Ani,shi ne ya tabbatar da ajiye aikin shugaban ga manema labarai da a Abuja ,inda yace shugaban ya ajiye aikin nasa a sakamakon dalilai na rashin lafiya.

Ani ya kara da cewa hukumar za ta fitar da sanarwa a hukumance dangane da Al'amarin.

Idan  ba a manta ba,Wata majiya daga hukumar ta bayyana wa manema labarai cewa an rubutwa shugaban kasa Muhammadu Buhari takardar ajiye aikin nasa kuma tuni aka amince da hakan.

Nan kuma Wata  kungiyar farar  hula  mai rajin tabbatar da bin doka da bada shawarwari mai suna RULAAC a takaice, Ta   yaba da murabus din da  Musliu Smith  yayi daga  kan matsayin Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Sanda ta kasa.

Rahotanni sun baiyana  cewa Smith ya yi murabus ne a ranar Laraba sakamakon shawarar da kwamitin hukumar ya bayar.

A cikin  wata sanarwa da  kungiyar ta  fitar, Ta yi maraba da matakin da Musliu Smith ya dauka, inda aka maye  gurbinsa da mai shari’a  Clara Ogunbiyi mai ritaya, wadda  ta kasa   kwamishiniyar shari’a a hukumar.

Shugaban kungiuyar   Okechukwu Nwaguma  yace  sun sha nanata  cewar  nada tsohon sufeton yansanda na kasa  a matsayin shugaban hukumar kula da aiyukan yan sanda ta kasa, ya karya ka’idar doka  da kuma makusudin da yasa aka kafa hukumar.