On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Shugaban Hukumar Shirya Jarabawar JAMB, Yace Bai Kamata Malaman Jami'oi Su Shiga Yajin Aiki Ba.

Magatakardan Hukumar Shirya jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta kasa, Farfesa Ishaq Oloyede, Ya baiyana matakin tafiya yajin aiki da Kungiyar Malaman jami’oi ta kasa ASUU ta dauka, a matsayin abunda bai zama wajibi ba.

Oloyede  ya baiyana haka ne lokacin da yake gabatar da wasu kayayyaki na mIlyoyin Naira  ga  Asibitin koyarwa  na Jami’ar Ilorin  domin inganta harkokin lafiya, Wanda  Hukumar ta samar hadin gwiwa  da kasar Amurika.

A cewarsa  yawan tafiya yajin aiki da Manyan Makarantun kasar nan keyi shine babban abunda ya kara illata Dalibai da kuma kasa Baki Daya.

Sauran Cibiyoyin kiwon Lafiyar da suka amfana  daga  tallafin, sun hada  da Asibitin koyarwa  na Maiduguri   da Asibitin koyarwa na jami’ar Yusuf Maitama Sule  dake nan Kano,  da kuma wasu  Asibitoci  9 dake shiyyoyi 6 na  kasar nan.