On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Shugaban Kasa Buhari Ya Ce Najeriya Tana Zaune Cikin Koshin Lafiya

SHUGABAN KASA BUHARI

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kasar nan tana zaune cikin koshin lafiya. Shugaban ya kawar da rade-radin cewat, rashin tsaro na karuwa a kasar nan a wasu bangarorinta .

Da yake jawabi a yayin wani taro da aka gudanar a Abuja ta bakin mai magana da yawunsa, Femi Adeshina, shugaba Buhari ya bayyana cewa an shawo kan matsalar rashin tsaro da ake fuskanta a sassan kasar.  

A cewarsa, Sanarwar da wasu kasashen duniya suka fitar akan sha’anin tsaron kasar nan, sam abun ba haka yake ba.

A nan kuma, Jami’an tsaro na rundunar CIVIL DEFENCE  sun bayyana cewa, an dauki dukkanin matakan da suka dace domin kawar da dukkanin wata matsala ta rashin tsaro a kasar nan.

Babban Kwamandan rundunar Ahmed Audi, ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen cimma wannan yunkuri data sanya a gaba.

Dagan an sai ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da duk wasu rade rade da ake yi na  kalaman da wasu keyi da nufin bata sunan kokarin gwamnatin tarayya na yaki da rashin tsaro a kasar fadin kasar nan.