On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Shugaban Kasa Buhari Ya Kaddamar Da Aikin Hakar Rijiyar Mai A Jihar Nasarawa

BUHARI

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin hakar rijiyar mai a karamar hukumar Obi ta jihar Nasaraw

Da yake jawabi jim kadan bayan kaddamar da aikin  ta hanyar  allon gani gaka a ranar Talata, Shugaba Buhari ya baiyana fatan cewar  sabon aikin  zai temaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa da inganta rayuwar  daukacin ‘yan Najeriya.

Kazalika ya yi kira ga kanfanin sarrafa albarkatun mai  na kasa  da ya tabbatar da cewar  aikin hakar  rijiyar danyen mai  bai haifar da wasu matsaloli  ga  yankunan da suke wajen ba.

Shima a nasa bangaren, karamin ministan albarkatun mai na kasa,Timpre Sylva,  ya  ce aikin hakar  rijiyar man  zai  temaka wajen samar da  arziki ga jama’ar jihar Nasarawa da kuma kasa baki daya.