On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Shugaban Kasa Buhari Ya Tashi Daga Madina Zuwa Birnin Makka Domin Yin Umrah

Buhari A Madina

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi daga birnin Madina zuwa birnin Makkah na kasar Saudiyya, a ci gaba da ziyarar aiki ta kwanaki takwas da ya ke yi a kasa mai tsarki.

A lokacin da yake birnin Madina, shugaban  kasar ya ziyarci wuraren tarihi na addini da suka hada da wani  babban  wajen  bikin baje koli na kasa da kasa na kayayyakin  tarihin Annabi  Muhammad  Sallalahu Alaihi Wasalam.

Ya kuma yi salloli biyar da kuma sallar tarawihi a masallacin Annabi dake birnin Madina  kafin ya tashi zuwa Makkah  daren jiya  Laraba.

Ana sa ran shugaban kasa zai yi gabatar da ibadar  umarah da  zarar  ya sauka birnin na Makkah a daren jiya.