On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Shugaban Kasa Buhari Ya Umarci Dakarun Soji Su Tabbatar Sun Kakkabe Yan Ta'adda Daga Doron Kasa

Shugaba Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci dakarun sojin kasar nan dasu tunkari yan ta’adda sannan kuma su tabbatar sun kakkabe su daga kan doron kasa.

Shugaban kasar ya bayar da wannan umarni ne, a barikin sojoji ta Jaji dake jihar Kadunam lokacin da yake gabatar da jawabi, a yayin bukin yake dalibai 247  na kwalejin rundunar soji ta kasa.

Yace shekaru 12 da suka wuce Najeriya na cikin kalubale na barazanar rashin tsaro  daya  addabi kasar nan.

Ya  kara da cewa kasar nan zata yi amfani da karfin ikon da take dashi domin tabbatar da tsaro da adalci da kuma wanzuwar zaman lafiya tare da hadin kan kasa da samun cigaba mai dorewa da kuma  tabbatar da kimar da take dashi a kasashen duniya.

 

 

 

More from Labarai