On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Shugaban Kasa Buhari Zai Tafi Landan A Yau Domin A Duba Lafiyarsa

shugaban kasa Buhari

Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari zai tafi birnin London na kasar Burtaniya a yau din nan domin a Mai magana da yawun shugaban kasa , Femi Adesina shine ya wallafa haka a shafinsa na Twitter ya ce ana saran Buhari zai dawo gida Najeriya a cikin mako na biyu na watan Nuwamba mai kamawa.

Shugaban kasar ya sha tafiya Landan domin duba lafiyarsa tun lokacin da ya fara mulkin kasar nan.

A 2017, Shugaban ya kwashe kwanaki 150 a Burtaniya a wata tafiyar duba lafiyar da ba a bayyana abin da ke damun shi ba.

Buhari ya kara komawa Burtaniya a watan Mayun 2018 domin ganin liktansa, inda ya yi kwana hudu kacal a kasar.

Kazalika  a  watan  Nuwambar 2020 ne, mai dakin shugaban kasa Aisha Buhari, ta ce akwai bukatar inganta bangaren lafiya a Najeriya domin a rage tafiye-tafiyen neman magani kasashen waje