On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Ce Wuce Makadi Da Rawa Ce Ta Sa Jam'iyyun Hamaiyya Shan Kaye

BUHARI

To manyan zabukan kasar nan dai sunzo kuma sun tafi, Sai dai kuma har yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari na cigaba da taba alli kan babban dalilin da yasa manyan jam’iyyun hamaiyya suka sha kaye a zaben.

A cewarsa  a yayin da jam’iyyar  APC  ta dage  domin ganin ta rike kujerar  shugaban kasa,Su kuwa jam’iyyun hamaiyya  sun dogara ne  da shacin fadin da ake  na cewar jam’iyya mai mulki  ba zata ci  zabe  ba, wanda  hakan suka sakankance.

Shugaban kasar  ya baiyana haka a  jiya,Yayin ganawarsa da gwamnonin jam’iyyar  APC  a fadarsa dake Abuja, Ya  ce  jam’iyyarsa ta APC  ta zage  damtse inda  ta yi ba dare  ba rana  tare kuma da yin taka tsan-tsan  domin ganin ta samu nasara a zaben.

Kazalika shugaban kasar  ya  jaddada  cewar manyan jam’iyyun  hamaiyya sunsha kaye a zaben shugaban kasar  nan, saboda wuce  makadi  da rawa, Sannan kuma  ya  kalubalance su kan yadda suka ki  amincewa  da shan kaye.