On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Gana da Abokan Karatunsa na Firamare da Sakandire

Abokan Karatun Buhari

Kazalika Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi tadi tare da abokna karatun nasa inda suka tuna baya.

Shugaban kasar  yaje  Mahaifarsa dake garin Daura a jihar Katsina a ranar Juma’a domin  gudanar da shagalin  Babbar  Sallah, kuma tun daga ranar yake a can.
A rana ta hudu ne abokan Karatun nasa, suka kai masa ziyarar  barka da  Salla, kamar yadda yake kunshe cikin wata sanarwa da Kakakinsa Malam Garba shehu ya fitar.
Kazalika Abokan Karatun nasa sun bawa shugaban kasar kyauta sannan kuma aka dauke su hoto tare a matsayin na tarihi.