On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Shugaban Kasa Ya Dakatar Da Shugaban Hukumar Sufurin Jiragen Sama Ta Kasa

Kyaftin Nuhu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Shugaban Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta kasa NCAA, Kyaftin Musa Shuaibu Nuhu, ba tare da bata lokaci ba

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar, ta ce dakatarwar ita ce  zata  baiwa hukumar EFCC damar gudanar da bincike kan ayyukan shugaban hukumar da aka dakatar da sauran manyan jami’an hukumar  kula da sufurin jiragen sama ta kasa  NCAA.

Shugaban ya umurci Kyaftin Chris Najomo da ya fara aiki a matsayin mukaddashin  shugaban Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta kasa  a nan take.

Shugaban ya kuma umurci Ministan Sufurin Jiragen Sama da ya fara shirin daukar  Shugaban Jami’ar da sauran manyan jami’an  gudanarwa  na Jami’ar koyar da harkokin  Sufurin Jiragen Sama  ta Afrika da aka samar a  nan Najeriya.

Bugu da kari  shugaban kasar  ya sauke  wasu  shugabanni da kuma daraktoci  guda  shida dake  hukumomi daban daban  na ma’aikatar  sufurin jiragen sama  ta kasa, tare  da maye gurbinsu da wasu.