On Air Now

Off Air

Noon - 6:00pm

Za'a Magance Matsalar Rashin Wadatuwar Kudi Nan Da Mako Daya Inji Buhari

BUHARI

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ya bukaci al'ummar kasar nan dasu bashi kwanaki Bakwai domin kawo karshen matsalolin kudi da al'ummar kasa suke a ciki, biyo bayan sauyin takardun kudi na naira da babban bankin kasa ya bullo dashi.

Shugaban kasar na  wannan  kalaman ne a  yayin da kungiyar  gwamnonin jam'iyyar APC suka kai masa ziyara a  fadarsa dake Villa,  inda suka baiyana  cewa  yanayi da ake ciki na zama  babbar  barazana ga   nasarorin da gwamnati mai ci ta samu a bangaren  daga likafar  fannin tattalin arzikin kasa.

Sai dai shugaban kasar  ya  baiyana  cewa  sauya  fasalin takardun kudin da aka yi zai samar  da cigaba  ga  bangaren  tattalin arzikin kasa, yana  mai baiyana shakkunsa  kan  yadda  Bankuna  ke nuna kokontonsu wajen samun nasarar  shirin.

Ya kara da cewa  wasu bankunan  sun damu ne kawai da kansu , kuma koda  an kara masu shekara  daya , ba  za'a samu  magancewar  matsalar ba, saboda  son  zuciyarsu.

Kazalika shugaban kasa Muhammadu Buhari  ya ce  ya kallin halin da al'umma  suke  ciki  dangane da karancin kudin naira  ta  Akwatin Talabijin, kuma kwanaki goma da aka  kara  zai  magance  tsananin da al'ummar suke dashi.