On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Shugaban Kasa Zai Gabatar Da Kasafin Kudin 2023 A farkon Makon Watan October

SHUGABAN KASA BUHARI

Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, Ya baiyana cewa, ana saran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kudirin kasafin kudin badi a gaban zauren majalisar dokokin ta kasa, a farkon makon watan Oktoban bana.

Kakakin majalisar ya baiyana haka ne lokacin da yake yiwa manema Labarai  jawabi, jim kadan bayan kammala  duba  dakunan taron  sauraron ra’ayoyin  jama’a  na  28 da kuma  234  da  majalisar zata yi amfani dasu a matsayin na wucin gadi  wajen rika gudanar da zamanta na yau da kullum, a sakamakon gyare-gyaren da ake kan yiwa zaurin majilar wakilan a halin yanzu.

Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na Jagorantar taron Majalisar Zartawa na kasa

Yace  za’a kammala saita wurin da majalisar  zata rika amfani dashi a matsayin zauren ta na wucin gadi gabanin ranar  20 ga watan da muke ciki, lokacin da majalisar  zata koma bakin aiki.

Femi Gbajabiamila ya kara da cewa, aikin gyara majalisar zai fi amfanar  sabbin yan majalisa masu zuwa  kasancewar  ba zai kammala ba har cikin watan Augustan badi.