On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Shugaban Kasar Amurika Ya Fadi Kasa Lokacin Da Yake Jawabi

JOE BIDEN

Shugaba Joe Biden ya fadi akan wani dandamalin gabatar da jawabi a yayin wani taro da aka gabatar a Kwalejin horas da Sojojin Sama da ke Colorado, sai dai rahotanni sun baiyana cewar bai ji wani ciwo ba.

Shugaba  Biden, mai shekara 80, Ya gabatar da jawabin sa  ga   daliban da suka kammala makarantar   horon  sojin saman  ne, inda  ya yi musabaha  da daya  daga cikin daliban  wanda  ya  girgiza  hannunsa, amma  lokacin da zai koma kan kujerarsa  daga dandamalin sai  ya  fadi.

Jami’an rundunar sojin sama sun taimaka masa wajen dawo da shi  kan kujerar.

Biden shi ne mutum mafi tsufa da ya taba zama shugaban kasar  Amurika   kuma  yanzu haka, yana neman wa'adi na biyu a zaben shekarar  2024. Rahoton likitansa na wannan shekara ya nuna cewa yana cikin koshin lafiya kuma yana motsa jiki akai-akai.