On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Shugaban Kasar Turkiyya Erdogan Ya Dakatar Da Yakin Neman Zabe Saboda Rashin Lafiya

ERDOWAN NA TURKIYYA

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya dakatar da yakin neman zabe bayan wata rashin lafiya da ya kamu da ita a lokacin da ake wata hira da shi kai tsaye a gidan talabijin inda aka dakatar da gabatar da hirar ba zato ba tsammani.

Bayan hutun mintuna 20, Shugaban kasar  ya sake  dawo wa  hirar  inda  ya baiyanawa  jama’a  cewar  yana  fama da ciwon ciki  mai tsanani.

Erdogan mai shekaru 69, na fuskantar yakin neman zabe mafi zafi a  kasar,  yayin da aka zabi babban madugun adawa Kemal Kilicdaroglu domin ya tsayawa takara a rukunin   wasu  jam'iyyun siyasa shida  inda  zai kara  da shugaban kasar.

Sai dai kuma jagoran  yan hamaiyyar  na daga cikin jiga-jigan 'yan adawa da suka yi wa shugaban fatan samun sauki cikin gaggawa.