On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Shugaban Kungiyar Kabilar Igbo George Obiazor Ya Mutu

George Obiazor

Shugaban kungiyar Al’ummar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo, Farfesa Geroge Obiazor ya mutu, Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma ne ya tabbatar da mutuwar tasa ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Instagram a daren jiya.

Ya baiyana mutuwar  jagoran Igbon kuma  tsohon jakadan kasar nan  a  Amurika, da kasar Banu Isra’ila  a matsayin babban rashi  ga  al’umma jihar Imo da shiyyar kudu maso  gabashin kasar nan da kuma  kafatanin Najeriya.

Gwamnan jihar Imo  ya baiyana cewa, Iyalansa  zasu sananar  da lokacin da  za’a yi bikin binne  marigayin,  Dama  tun da  sanyin safiyar ranar Laraba ne, aka  fara yada  jita-jitar  mutuwar  shugaban kungiyar   Kabilar  Igbon.