On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Shugaban Najeriya Tinubu Ya Bada Umarnin Farautar Maharan Jihar Plato

An umarci jami’an tsaro da su gaggauta bankado kowane lungu da sako na kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na jihar Plato da nufin kamo ‘yan bindigar da suka kashe mutane da dama a yankin.

Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin a wata sanarwa ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale a ranar Talata.

Haka kuma shugaban ya ba da umarnin a gaggauta kai kayan agaji ga wadanda abin ya shafa, da kuma kula da wadanda suka jikkata.

A yayin da yake yin Allah wadai da hare-haren ta'addanci, munanan ayyuka da rashin tausayi, Shugaba Tinubu ya jajantawa gwamnati da al'ummar jihar Plato, ya kuma tabbatarwa 'yan Najeriya cewa wadanda suka aikata kisan, na bakin ciki ba za su tsira daga shari'a ba.