On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Shugaban Najeriya Tinubu Zai Halarci Taron G20 A India

A yau Litinin shugaba Bola Tinubu zai tafi birnin New Delhi na kasar India domin halartar taron shugabannin kasashen G-20, kamar yadda mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya tabbatar.

A wata sanarwa da ya fitar a karshen mako, Ngelale ya ce shugaban zai bar Abuja ne domin halartar taron a India bisa gayyata ta musamman da firaministan India, Narendra Modi ya yi masa.

Ana saran taron zartaswar zai samu halartar manyan masu masana'antu da sauran kamfanoni masu zaman kansu na India da  masana'antun Najeriya, da kuma manyan jami'an gwamnati na kasashen biyu.

Sanarwar ta kara da cewa shugaban zai dawo Najeriya bayan kammala taron.