Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta haramta duk wani nau'in bukukuwan kammala karatu na "Sign Out" da ɗalibai ke yi, tana mai bayyana cewa ba za ta lamunci duk wani abu da ya saɓa wa koyarwar addinin Musulunci ko ɗabi'un al'umma ba.
Hukumar ta ce haramcin ya haɗa da cudanya tsakanin maza da mata ta hanyar da ba ta dace ba, yaga kayan makaranta, rubuce-rubuce a jikin kayan makaranta, da sauran ayyukan da ake ɗauka a matsayin rashin ɗa'a yayin bukukuwan kammala karatu.
A cikin wani saƙon murya da ya aike wa Arewa Radio ta manhajar WhatsApp, Mataimakin Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Mujahedeen Aminuddeen, ya ce hukumar ta tura jami'an ta zuwa dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar domin tabbatar da aiwatar da umarnin.
Ya bayyana cewa za a gudanar da wannan sintiri ne a ranar Alhamis, lokacin da ake sa ran ɗalibai za su rubuta jarabawarsu ta ƙarshe, tare da gargaɗin cewa duk wanda aka samu ya karya wannan doka za a kama shi kuma a ɗauki matakin da doka ta tanada a kansa.
A wani labari makamancin wannan, shugaban Karamar Hukumar Dawakin Kudu, Alhaji Sani Ahmed Mai Rago, ya sanar da haramta gudanar da wadanann bukukuwan.
Shugaban ya ce an dauki wannan mataki ne domin kare tarbiyyar matasa da ɗalibai, tabbatar da zaman lafiya, tare da hana duk wani abu da ka iya haifar da rashin ɗa'a ko tayar da hankalin jama'a.
Ya yi kira ga iyaye, shugabannin makarantu, malamai, masu ruwa da tsaki da kuma matasa da su bi wannan umarni tare da bai wa gwamnati hadin kai wajen tabbatar da doka da oda.
Alhaji Sani Ahmed Mai Rago ya kuma gargadi cewa duk wanda aka samu ya karya wannan umarni zai fuskanci matakin doka daga hukumomin tsaro da sauran hukumomin da abin ya shafa.
Comments
Add a comment