On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Sojoji Da 'Yansanda Sunja Kunnen Masu Shirya Zanga-Zanga

YAN SANDA

Gabanin yanke hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa dake zamanta a Abuja, zata yi a gobe Laraba, Dakarun sojin kasar da kuma jami’an ‘yansanda sun baiyana cewar ba zasu saurarawa duk wani mutum dake shirin tada zauni tsaye, ta hanyar daukar doka a hannunsa.

Daraktan yada labaran rundunar sojin kasa, Birgediya janar Tukur Gusau, Ya gargadi masu shirin tada zauni tsaye a gobe, da su yi gaggawar janye aniyar tasu.

Ya ce dakarunsu  tare da hadin gwiwar  jami’an tsaro  ba zasu saurarawa  duk wanda aka samu  da yunkurin haifar da wata fitana  ba.

Haka suma  Hukumomin ‘yansanda  sun sake tsaurara matakan tsaro a jihohinsu gabanin  yanke hukuncin da kotun zata yi a ranar Larabar nan.