On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Sojoji Sun Kifar Da Gwamnatin Mohammed Bazoum

NIJAR

Dakarun sojin jamhuriyar Nijar sun kifar da gwamnatin Mohammed Bazoum.

Wadansu sojoji kalilan ne suka  sanar da yin juyin mulkin ta  gidan Talabijin na kasar a daren jiya,  Yan  sa’oi  bayan da sojojin suka  yiwa  shugaban kasar  daurin tala-la a gidansa dake  fadar shugaban kasa.

Kazalika sun sanar da rushe kundin tsarin mulkin kasar  da  kuma  dukkanin wasu  hukumomi da ma’aikatun gwamnati, tare da  kulle  iyakokokin shige da fice  na kasar,  inda  suka baiyana cewar  sunyi juyin mulkin ne saboda halin tabarbarewar  shugabanci da kasar  ta tsinci kanta a ciki.

Da yake karanta  sanarwar  yin juyin mulkin, Kanal  Amadou Abdramane, wanda  wasu sojoji guda tara suke zagaye  da  shi,  Ya  ce  sojoji  sun kwace  mulkin jamhuriyar  Nijar.