On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Son Zuciya Ne ASUU Ta Nemi Albashin Wata 6 Daga Gwamnati Yayinda ‘Dalibai Ke Zaune A Gida - Kungiyoyi

Wasu kungiya mai rajin kare dimukuradiyya da neman cigaba sun yi Allah-wadai da matakin da mambobin kungiyar malaman jami’oi ta kasa ASUU suka dauka na ajiye dalibai a gida tare bijiro da bukatar a biyan albashin wata shida duk da cewa suna zaune a gida.

A makon jiya ne ministan ilimi Malam AdamuAdamu ya yi barazanar cewa mambobin kungiyar ba za su samu albashi ba tsawon watannin da suka kwashe suna yajin aiki.

Sai dai ASUU ta ce mambobinta za su fara koyarwa ne daga matakin zangon karatu na 2022 zuwa 2023 sannan ba zasu nsaurari sauran zangon da ba a kammala ba a lokacin yajin aikin, idan gwamnati ta gaza biyan su hakokin da suke nema.

Sai dai kungiyoyi masu zaman kansu, a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar jiya, ta nuna rashin jin dadin ta kan yadda malaman jami’oin ke ci gaba da tsare daliba a gida saboda neman kudin da ba su yi aiki ba.

Mohammed Umar Salihu, shugaban kungiyar NPI da Akinloye James, shugaban ISD, sun bayyana bukatar da ASUU ta bijiro da ita ta neman albashin watannin da mambobinta ke yajin aiki a matsayin son zuciya..