Mikel Merino, wanda ya shigo daga benci, ne ya zura ƙwallon da ta bai wa Spaniya nasarar doke Portugal da ci 1-0 a ƙarshen wasan zagaye na biyu, tare da tabbatar da tikitin zuwa zagayen ukun karshe, wanda ya kuma kawo ƙarshen tafiyar Cristiano Ronaldo a gasar Kofin Duniya a ranar Litinin.
Bayan wannan nasara, kasar Spaniya, wadda ta taba lashe gasar cin kofin duniyar za ta kara da Amurka, wadda ita ce kaɗai daga cikin ƙasashen da ke karɓar baƙuncin gasar da ta rage a fafatawar, ko kuma Belgium, a wasan zagaye na ukun karshe da za a buga ranar Juma'a a birnin Los Angeles.
A gaban dubban magoya baya 70,649 da suka cika filin wasan na ƙungiyar Dallas Cowboys mai dauke da na'urar sanyaya iska, wasan da aka yi hasashen zai kayatar, sai dai bai cika yadda aka zata ba.

Wannan sakamakon ya sanya wasan ya zama na ƙarshe ga Cristiano Ronaldo mai shekaru 41 a gasar Kofin Duniya. Ronaldo, wanda yanzu yake taka leda a Saudiyya, ya bayyana tun a jajibirin wasan cewa wannan ce gasarsa ta ƙarshe a babban dandalin ƙwallon ƙafa na duniya.
Ƙasashen biyu sun shiga wasan ba tare da sun yi rashin nasara ba a gasar. Sai dai yayin da Portugal ba ta nuna wata bajinta ta azo a gani ba a wasu wasannin, ita kuwa Spaniya ba a zura mata ko ƙwallo ɗaya a raga ba tunda aka fara gasar.
Duk da irin tarihin da ƙwarewar da ƙasashen biyu suke da shi a wasan ƙwallon ƙafa, sau ɗaya kacal Spaniya ta taɓa lashe gasar cin Kofin Duniya, a shekarar 2010, yayin da mafi kyawun sakamakon da Portugal ta samu shi ne matsayi na uku da ta samu a shekarar 1966.

Kafin wasan, an mayar da hankali sosai kan fafatawar tsakanin Cristiano Ronaldo da matashin ɗan wasan Barcelona mai shekara 18, Lamine Yamal, inda aka bayyana wasan a matsayin haɗuwar fitattun 'yan wasa biyu da ke wakiltar farkon da kuma ƙarshen manyan sana'arsu a fagen ƙwallon ƙafa.
Comments
Add a comment