On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Super Falcons Ta Samu Tikitin Gasar Cin Kofin Kwallon Kafar Mata Ta Duniya

Tawagar Super Falcons

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta kasa, Amaju Pinnick, Ya yaba da kwazon da tawagar yan wasa mata ta kasa, Super Falcons suka nuna, bayan nasarar da suka samu ta tikitin shigar gasar cin kofin kwallon kafar mata ta duniya ta shekarar 2023.

Kungiyar Super Falcons ta doke  kungiyar Indomitable Lionesses ta kasar Cameroo da ci 1 tak mai ban haushi a wasan kusa dana karshe  da suka yi  a daren jiya,  a cigaba da buga wasan cin kofin nahiyar afrika  na mata da ake yi a kasar Moroco.

Najeriya wadda  ta dauki kofin gasar har sau 9 na fatan ganin a wannan karon ma  ta  daga  kofin gasar a karo  na 10 a kasar  Morocco.