Kamata yayi nakuda ta kasance wata muhimmiyar tafiya ta kawo rai duniya, sai dai ga mata masu juna biyu da dama a kauyen Mai Unguwa da ke karamar hukumar Dambatta a Jihar Kano, tana farawa ne da neman adaidaita sahu cikin gaggawa domin tafiya zuwa babban Asibitin Dambatta, duk da irin hadarin da ke tattare da tafiyar.
Hakan na faruwa ne saboda ana rufe cibiyar lafiya daya tilo da al'ummar kauyen suke dogara da ita da karfe uku na rana, sakamakon karancin ma'aikata da kuma rashin kayan aiki. Wannan na tilasta wa mata masu juna biyu zabi tsakanin yin tafiyar mai hadari ko kuma haihuwa a gida.
A wannan makon, Victor Christopher ya ziyarci kauyen Mai Unguwa, inda mazauna suka ce lalacewar cibiyar lafiyar na tilasta wa mata masu juna biyu jefa rayuwarsu cikin hadari, yayin da Gwamnatin Jihar Kano ke cewa tana fadada shirin samar da cibiyoyin lafiya masu aiki sa'o'i ashirin da hudu.
Yayin da wasu mata a kauyen Mai Unguwa suka tsallake rijiya da baya suka kuma samu sukunin ba da labarin wahalhalun da suka sha kafin haihuwa da kan su, Nana Asma'u bata samu wannan damar, wadanda ta bari ne suka iya bada labarin nata.

Mijinta, Iliyasu Isyaku, ya ce Nana ta shafe sa'o'i tana nakuda bayan ruwanta ya fashe da misalin karfe uku da rabi na dare, bayan cibiyar lafiyar al'ummar ta dade da tashi daga aiki. Ya ce ita da jaririn da ke cikinta sun rasu kafin ma likitoci su kai kanta saboda wahalhalun hanya, jim kadan bayan isar su babban asibitin na Danbatta.
Ba kowanne iyali ne ya rasa wani nasa ba, amma da dama har yanzu suna dauke da abubuwan firgici da suka fuskanta a cibiyar lafiyar da ta lalace.
Zainab Jamilu ta tuna lokacin da take zaman awo, inda wani bangare na rufin ginin ya fado kasa, dan taki kadan daga inda take zaune ba.
Irin wadannan abubuwa sun sa mata da dama daina zuwa cibiyar domin awon ciki, inda jami'in lafiya mai aikin sa kai, Sani Bashiru Mukhtar, ya ce yawan masu zuwa ya ragu matuka, har ta kai ga wa’adin wasu magunguna na karewa ba tare da an yi amfani da su ba.

Saboda damuwa da halin da ake ciki, Shugaban Kungiyar Cigaban Kauyen Mai Unguwa, Atiku Sulaiman, ya ce sun sayi katinan asibiti dubu daya domin karfafa wa mazauna gwiwar neman kulawar lafiya.
Sai dai ya ce duk da koke-koken da suka sha kai wa hukumomi, har yanzu ba a samu wani gagarumin sauyi ba.
An gina cibiyar lafiyar kimanin shekara ashirin da suka gabata, amma yanzu ta lalace matuka. Bangon ginin ya tsage, wanda ya zama mafakar kadangaru da sauran dabbobi masu ruf da ciki, yayin da kashin jemagu ya bazu a wasu sassan ginin.
Baya ga haka, cibiyar ba ta da muhimman kayan aiki, kuma tana aiki na tsawon sa'o'i biyar kacal a rana, duk da cewa tana yi wa mata masu juna biyu daga kauyen Mai Unguwa da makwabtansu hidima.

Daya daga cikin mazauna kauyen, Rabi Nura, ta ce ta kuduri aniyar zuwa Asibitin Kwararru na Dambatta idan nakuda ta same ta, saboda cibiyar lafiyar ba ta karbar haihuwa.
A cewar Hukumar Kula da Lafiya ta Matakin Farko ta Kasa, a shekarar 2024 Najeriya na rasa kusan yara 2,300 'yan kasa da shekara biyar da kuma mata 145 masu shekarun haihuwa a kowace rana.
Ko da yake Gwamnatin Jihar Kano ta ce mace-macen mata masu haihuwa sun ragu daga 1,025 zuwa 570 cikin mata 100,000 da suka haihu sakamakon matakan da ta dauka, mazauna kauyen Mai Unguwa sun yi imanin cewa inganta cibiyar lafiyarsu zai kara rage mace-macen da za a iya kauce musu.
Mai unguwar Kauyen Mai Unguwa, Garba Alhassan, ya ce bai kamata mace mai juna biyu ta rika yin tafiya mai nisa domin haihuwa ba saboda rashin ingantacciyar cibiyar lafiya a cikin al'umma, inda ya roki gwamnatin jihar da ta inganta cibiyar domin ta rika ba da hidima sa'o'i ashirin da hudu a kowace rana.
Da yake mayar da martani, Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce gwamnati ta riga ta inganta cibiyoyin lafiya 320, kuma tana shirin fadada aikin zuwa cibiyoyi 484 da ke dukkan mazabun siyasar jihar.
Ya ce cibiyoyin da aka inganta za su rika aiki sa'o'i ashirin da hudu domin kara samar da kwararrun masu karbar haihuwa da kuma rage mace-macen mata da kananan yara.
Ga mutanen Kauyen Mai Unguwa, mafitar ba ta da wahala, abin da suke fata shi ne mace ta gaba da nakuda ta same ta ta tarar da ma'aikacin lafiya yana jiranta, ba kofar da aka kulle ba.
Comments
Add a comment