On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Takaddama ta Sake Barkewa akan Takarar Musulmi da Musulmi

Shawarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na cigaba da rike Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 ta sake tayar da muhawara kan tikitin Musulmi da Musulmi na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kungiyoyi da dama, musamman daga Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu, sun bayyana rashin amincewarsu da matakin.

Kungiyar Coalition of South East Youth Leaders da South-South Youths Initiative sun ce cigaba da amfani da tikitin Musulmi da Musulmi na iya kara rarrabuwar kawuna a kan addini tare da sanya wasu sassan kasar su ji an ware su daga shugabancin kasa.

Shugaban kungiyar Middle Belt Forum na kasa, Dakta Pogu Bitrus, shi ma ya soki matakin, inda ya ce kamata yayi jam'iyyar APC ta yi la'akari da zabar Kirista daga Arewacin Najeriya a matsayin mataimakin dan takara domin karfafa hadin kai da tabbatar da daidaito tsakanin al'ummomin kasar.

Sai dai shugaban kungiyar Centre for Accountability and Open Leadership (CAOL), Debo Adeniran, ya kare matakin shugaban kasa, tare da cewa irin fargabar da aka nuna kafin zaben 2023 ba ta tabbata ba bayan kafa gwamnati, yana mai cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne kwarewa da iya gudanar da mulki ba addinin dan takara ba.

Adeniran ya kuma ce cigaba da rike Shettima na iya kasancewa sakamakon amincewar da Shugaba Tinubu ke da ita da shi, da kuma irin kyakkyawar alakar aiki da suka gina tun bayan hawansu mulki a shekarar 2023.

Tun a zaben 2023 ne APC ta tsayar da Bola Tinubu da Kashim Shettima a matsayin 'yan takarar shugaban kasa da mataimakinsa duk da ce-ce-ku-cen da tikitin Musulmi da Musulmi ya haifar.

Yayin da jam'iyyar ke shirin tunkarar zaben 2027, batun ya sake zama abin muhawara tsakanin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar Najeriya.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thunder storm

    High: 33°C | Low: 23°C