On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Tayar Jirgin Max Air Ta Fashe A Lokacin Da Zai Sauka A Abuja

Tayar Jirgin Max

Wani jirgin kanfanin Max Air da ya taso daga birnin Yolan jihar Adamawa a ranar Lahadi yayi gaggawar sauka,wanda hakan yayi sanadin soke tashin jiragen sama da dama da kuma jinkir ta tashin wasu.

Mafi  akasarin jiragen da abun ya shafa  sune  wadanda  basa  sauka  idan dare ya  yi,  A  yayin da  kanfanin jirgin sama na Air  Peace  ya sanar da  soke  tashin  jiragensa  da  dama, kamar  yadda  ya aike da sakon kar  ta  kwana  ga  Fasinjojinsa.

Kazalika  sauran wasu  kanfanonin sun soke  tashin  jiragensu, lamarin  da  ya  sa matafiya  da dama  suka  makale a  filin jirgin saman Abuja.

Saukar  gaggawar da jirgin ya  yi, tasa  an  dan rufe  titin da  ya  sauka  na dan wani lokaci  a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe  dake Abuja, Kafin jami’an bada agajin gagagwa su kaiga dauke  jirgin  sannan kuma  aka  gyara wajen  da abun  ya faru.

Rahotanni sun baiyana cewar  tayar  jirgin ce  ta  fashe  a daidai  lokacin da jirgin ke kokarin sauka, Lamarin da  ya sashi yin saukar ba zata, amma ba’a samu asarar  rai ba.

Mai magana  da  yawun hukumar  kula da filayen jiragen sama ta kasa,Uwargida  Faithful Hope  Ivbaze, ta  tabbatar da janye  jirgin  daga wajen da  ya sauka da karfe  8 da kwata  na dare, a  yayin da yanzu haka aka  fara yin bincike.