On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Tinubu Bai Gana Da Gwamna Wike A Faransa Ba.

TINUBU DA GWAMNA WIKE

Mai Magana da Yawun Dan Takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, Ya baiyana cewa Babu wata ganawa da aka yi tsakanin uban gidansa da kuma gwamnan jihar Ribas Nyesom wike a kasar Fransa a ranar Juma’a.

Wasu rahotanni da suka rika zagayawa sun baiyana yuyuwar  yin ganawa ta musamman a tsakanin Tinubu da Gwamna Wike wanda yasha kaye a zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

To sai dai a wata sanarwa da Kakakin Tinubu, Tunde Rahman ya fitar, Ya baiyana rahotannin a matsayin na kanzon kurege, Inda ya baiyana cewa kamar yadda aka sanar a baya, Bola Tinubu yaje kasar Faransa ne domin gabatar da wasu aiyuka na musamman, kuma zai dawo kasar nan, nan bada jimawa ba.

Kazalika shima wani dan kwamitin Amintattun na jam’iyyar PDP, Alhaji Adamu Maina Waziri ya musanta rahotannin wanda ya baiyana a matsayin na zuki ta malli.