Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi ta'aziyyar tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, yayin cika shekara guda da rasuwarsa, yana mai cewa sauyinsa daga shugaban mulkin soja zuwa jagoran dimokuradiyya ya sanya ya zama mutum na musamman a tarihin siyasar Najeriya.
Tinubu, wanda Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya wakilta a wajen taron addu'ar tunawa da marigayin, ya ce gadon da Buhari ya bari ya wuce mukaman da ya rike, domin rayuwarsa ta nuna daidaito tsakanin kalamansa, ka'idojinsa da kuma halayensa. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai da Sadarwa a Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Stanley Nkwocha, ya fitar a ranar Litinin. Tinubu ya ce, "Shugaba Buhari ya sadaukar da duk abin da yake da shi ga wannan kasa ba tare da wata shakka ba. Ya yi hidima da jarumtaka, da yakini, da kishin kasa ba tare da tunanin abin da kasar za ta ba shi a madadin haka ba." Da yake tuna shekarun da suka yi tare a siyasa, Tinubu ya bayyana Buhari a matsayin abokin tafiya wajen gina kasa da siyasar ci gaba. Ya ce, "Tun daga lokacin da ya kasance shugaban mulkin soja har zuwa sauyinsa zuwa jagoran dimokuradiyya kuma mai kare tsarin mulkin kasa, ya kasance abin koyi wajen kawo sauyi da gina kasa." Shugaban ya kara da cewa, duk da kalubale da ce-ce-ku-cen da suka rika dabaibaye mukamin shugaban kasa, Buhari ya ci gaba da samun amincewa da kaunar talakawan Najeriya bayan saukarsa daga mulki. A cewarsa, "Lokacin da ya sauke nauyin shugabanci har zuwa shekarun ritayarsa, amincewar talakawan Najeriya ba ta gushe daga gare shi ba. Ba kyauta ake ba mutum wannan amincewa ba, ana samunta ne ta hanyar rayuwar da ta cika da gaskiya, da rikon amana da daidaito tsakanin abin da mutum yake fada da abin da yake aikatawa." Tinubu ya yi kira ga abokan Buhari da masu goyon bayansa da su ci gaba da raya gadon da ya bari ta hanyar rungumar gaskiya, saukin kai da kuma da'a a rayuwarsu da ayyukan gwamnati. Ya ce, "Nauyin da ke kanmu a matsayin abokansa da makusantansa shi ne mu ci gaba da tafiyar da gadon da ya bari mana, wato gaskiya, saukin kai da rikon amana, tare da kokarin kai wa matsayin da ya kasance a rayuwarsa."
Comments
Add a comment