On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Tinubu Da Kashim Sunyi Nasara A Kotun Koli

Kotun Kolin ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa Atiku Abubakar suka daukaka a gabanta dake neman a soke cancantar takarar Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shattima na jam'iyyar APC.

A hukuncin da kotun mai alkalai biyar ta sanar a yau Juma'a ta ce jam’iyyar PDP ba ta da dama a doka ta yi kara akan al’amarin saboda acewar kotun PDP ba tad a hurumi a jam'iyyar APC.

Masu karar suna ikirarin cewa zaben Kashim Shettima a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu ya saba wa sassa na 29 (1) da  33 da 35  da kuma na 84 (1) (2) na dokar zabe  ta 2022.

A karar sun ce Shettima ya sabawa dokar saboda ya yi takarar mataimakin shugaban kasa da kuma kujerar majalisar dattawa ta Borno ta tsakiya a lokaci daya.

Saboda  haka ne wadanda suka shigar da karar suke neman kotun ta soke cancantar takarar APC da Tinubu da Kashin Shettima.