On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Tinubu Da Shattima Sun Karbi Ragamar Shugabancin Najeriya

Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu ya karbi rantsuwar kama aiki amatsayin sabon shugaban kasar Najeriya na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Tuni dai filin taro na Eagles square dake Abuja ya cika domin mika mulki mai cike da tarihi, kuma an tsaurara matakan tsaro sosai a wurin da ake  gudanar da gagarumin taron.

Alkalin Alkalan Najeriya mai shari'a Olukayode Ariwoola shine ya rantsar da Tinubu bayan rantsar da tsohon gwanan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima amatsayin sabon mataimakin shugaban kasa.

Tinubu ya kasance shugaban kasa na goma sha shida a jerin shugabannin Najeriya.

Sun tabbatar da  alkawarin yin biyayya ga kundin tsarin mulkin Najeriya tare da yin aiki ba tare da nuna son zuciya ba sannan suka sanya hannu a takardar rantsuwa.

Bikin na samun halartar manyan jami’ai na wasu manyan kasashen duniya kamar yadda  ofishin jakadancin Amurka ya sanar da isowar tawagar Amurka da shugaba Joe Biden ya aiko.

Shugaba Paul Kagame na Rwanda shima ya halarci  bikin mika mulkin haka kuma akwai  shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune baya ga shugaban jamhuriyar Nijar Muhammed Bazoum.