On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Tinubu Ya Aike da Kudirin 'Yan Sandan Jihohi ga Majalisar Wakilai

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisar Wakilai kudirin dokar gyaran Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999, domin samar da tubalin doka na kafa rundunar 'yan sandan jihohi a faɗin ƙasa.

A cikin wasiƙar da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya karanta a zaman majalisar na ranar Talata, Shugaba Tinubu ya roƙi 'yan majalisar da su ba kudirin kulawa ta musamman domin a gaggauta tantance shi.

Tinubu ya bayyana cewa kudirin na daga cikin muhimman tsare-tsaren gwamnatinsa na sake fasalin harkokin tsaro a ƙasar nan.

Ya ce idan aka amince da kudirin, zai samar da cikakken tanadin kundin tsarin mulki da zai bai wa jihohi damar kafa rundunonin 'yan sandansu, domin ƙarfafa matakan da ake ɗauka wajen fuskantar matsalolin tsaro da ke ƙara ta'azzara.

Shugaban ƙasar ya kuma ce kudirin ya ginu ne kan aikin da Majalisar Wakilai ta fara a baya, tare da ƙunsar wasu tanade-tanade da za su tabbatar da ingantaccen aiki da haɗin gwiwa tsakanin rundunar 'yan sandan tarayya da ta jihohi.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 33°C | Low: 23°C