On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Tinubu Ya Amince Ya Zabi Musulmi A Matsayin Mataimakinsa. Inji Ganduje.

TINUBU DA GANDUJE

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, Yace Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu Ya amince ya Zabi Musulmi a matsayin wanda zai yi masa takarar mataimaki.

Ya tabbatar da haka ne a ranar Juma’a, yayin wani taron addu’a na musamman da aka shirya wanda malamai 100 suka halarta a fadar gwamnatin jihar Kano. Gwamnan yace an bawa tinubu shawarar daukar musulmi a matsayin mataimakinsa, kuma ya amince da hakan.

Yace tsarin bayar da tikitin takarar shugaban kasa dana mataimakinsa ga musulmi kadai ba wani sabon al’amari ba ne a kasar nan, A bisa haka ne yayi kira ga malaman da su yiwa addu’ar zama  shugaban kasa a zabe mai zuwa.