On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Tinubu Ya Ce Abuja Ce Zata Cigaba Da Kasancewa Babban Birnin Taraiyya

BOLA TINUBU

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya musanta rade-radin da ake yi na cewar zai mayar da jihar Legas, babban birnin taraiyyar kasar nan, a maimakon Abuja, idan har aka zabe shi a kan matsayin shugaban kasa.

Ta cikin wata sanarwa da Majalisar yakin neman zaben shugaban kasa ta jam’iyyar  APC, ta fitar, Ta karya jita-jitar  tare  da yin  Allah  wadai da  ‘yan Hamaiyya  kan salonsu  na  bata suna a lokacin yakin neman zabe, da kuma ta’ba muhibbar dan takararsu na shugaban kasa.

Sanarwar mai dauke dasa hannun daraktan yada labarai da wayar da kai na majalisar yakin neman zaben, Bayo Onanuga, Ya  ce  Tinubu bashi da irin wannan shiri  kuma ba zai yi duk wani abu da  ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa ba.